Home NewsChina ta buƙaci Amurka ta daina bai wa Taiwan makamai

China ta buƙaci Amurka ta daina bai wa Taiwan makamai

China ta buƙaci Amurka ta daina bai wa Taiwan makamai tare da mutunta tsarinta na dunƙulalliyar kasa daya.

Wannan na zuwa bayan Amurka ta amince da sayar wa Taiwan da makamai na dala biliyan 11.

Makaman sun ƙunshi makaman roka da jiragen yaƙi marar matuka da kuma makamai masu linzami.

China ta ce za ta ɗauki matakan da suka dace na kare iyakokinta.

Wannan ne karo na biyu da Amurka ta sayar wa da Taiwan da makamai tun hawan Donald Trump shugaban Amurka karo na biyu.

You may also like

Leave a Comment