Home NewsHukumar Raya Arewa Maso Yamma NWDC Ta Gabatar Da Rahotan Ta 2025 A Gaban Majalisar Tarayya

Hukumar Raya Arewa Maso Yamma NWDC Ta Gabatar Da Rahotan Ta 2025 A Gaban Majalisar Tarayya

Shugaban hukumar, Farfesa Shehu Abdullahi Ma’aji, ne ya gabatar da rahoton a ranar Alhamis, wanda ya kunshi ayyukan da aka gudanar daga watan Janairu zuwa Disambar 2025, inda ya bayyana nasarorin da aka samu, matakan da aka dauka da kuma kalubalen da hukumar ke fuskanta, musamman rashin sakin kudade.
Kwamitin majalisar kan hukumar, wanda Sanata Babangida Hussaini da Suleiman Abubakar Gumi suke jagoranta, ya yaba wa shugabancin hukumar bisa irin ci gaban da aka samu duk da cewa ba a saki kudaden aikin ba.
Kwamitin ya amince da kyakkyawan tubalin da hukumar ta kafa, tare da alkawarin taimakawa wajen tura daraktocin zartarwa da daraktoci domin karfafa ayyukan hukumar.
Haka kuma, kwamitin ya bukaci hukumar da ta bai wa matsalar tsaro muhimmanci, la’akari da dokar ta baci da aka ayyana akanta.
Kwamitin ya kuma tabbatar da cewa za a saki kudin fara aiki nan take, domin bai wa hukumar damar fara ayyuka, hidimtawa jama’a da kuma tallafa wa mutanen da rikicin tsaro ya shafa domin sake dawo da su cikin al’umma.
Kwamitin ya shawarci hukumar da ta hada kai da gwamnatocin jihohi, masu zuba jari da kungiyoyin agaji domin karfafa ayyukanta.

You may also like

Leave a Comment