81
Wata babbar kotun tarayya a Abuja ta yi watsi da buƙatar neman beli da tsohon ministan Shari’ar Najeriya, Abubakar Malami ya yi domin sakin sa daga hannun hukumar EFCC.
Mai Shari’a Babangida Hassan ya ce bai zai iya amince wa da buƙatar belin ba saboda doka ta bai wa hukumar EFCC ta tsare tsohon ministan shari’ar domin ci gaba da bincike.
Tun dai ranar 8 ga watan Disamba Abubakar Malami ke tsare a wurin hukumar ta EFCC.
A ranar Laraba ne Malami ya kwarmata cewa jami’an hukumar sun kai samame ofishinsa da gidajensa da ke Abuja da Kebbi.
EFCC na riƙe da malami ne kan tuhumar laifuka guda uku waɗanda tsohon ministan ya musanta.
- Amfani da muƙami ba bisa ƙa’ida.
- Safarar haramtattun kuɗade.
- Laifuka masu alaƙa da kadarorin tsohon shugaban ƙasa, Sani Abacha da aka karɓo daga ƙasashen waje da suka kai dala miliyan 346.