Ta bayyana hakan ne yayin da take zantawa da manema labarai a gidan gwamnati na jihar Jigawa, inda ta jaddada muhimmancin tallafawa mabukata musamman a wannan lokaci na matsin tattalin arziki da ake ciki.
Ambasada Dakta Amina Umar Namadi ta ce, la’akari da halin kuncin rayuwa da ake fama da shi, ya zama wajibi mawadata su kara himma wajen tallafawa talakawa, musamman zawarawa da aka rasu aka barsu da yara.
Haka kuma, ta bayyana cewa gidauniyarta ta Hamdan Kaseeran Foundation ta samu nasarar tallafawa al’umma da dama, ciki har da zawarawa, marayu da sauran marasa galihu ta hanyoyi daban-daban.
A karshe, ta yi kira ga ’yan kasuwa da su ji tsoron Allah su kuma rangwanta farashin kayan masarufi domin saukakawa al’umma, musamman yayin da ake tunkarar azumin watan Ramadan.
66