Home NewsMajalisar malamai karkashin babban limamin Dawakin kudu,ustaz Umar tijjani umar,ta shirya taron fadakar da malamai na Dawakin kudu,

Majalisar malamai karkashin babban limamin Dawakin kudu,ustaz Umar tijjani umar,ta shirya taron fadakar da malamai na Dawakin kudu,

A yayin da ya rage kwanaki kadan kafin fara azumin watan Ramadan, Majalisar Limaman Masallatan Juma’a ta Jihar Kano, reshen karamar hukumar Dawakin Kudu ta gudanar da taron bita domin kara wa limamai kwarewa da shiri na musamman domin tunkarar watan mai alfarma.
Manufar taron ita ce zaburar da limamai kan yadda za su tsara hudubobi da tafsirai, da kuma jagorantar sallolin tahajjudi yadda ya kamata. Haka kuma an jaddada muhimmancin hada kai da jami’an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya a fadin karamar hukumar da ma jihar Kano State tare da yi wa kasa baki daya, wato Nigeria addu’o’in zaman lafiya da ci gaba.
Bugu da kari, an fadakar da limaman kan muhimmancin wayar da kan al’umma yadda za su ribaci falalar watan Ramadan, tare da kaucewa dabi’ar kin daukar azumi ko ajiye shi bisa hujjar rashin yarda da ganin wata. An bukaci limamai su jaddada hadin kai, biyayya ga hukunci da kuma bin ka’idojin addini wajen tabbatar da hadin kan al’umma.
Daga Abdullahi Adamu, wakilin Kano Live 24 a Dawakin Kudu.

You may also like

Leave a Comment