Home NewsGwamnatin Jihar Kano karkashin Ofishin Ambasada Maimunat Umar Sharif, Mai Bai wa Gwamna Shawara Kan Tsaron Al’umma haɗin gwiwa da Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kano sun gudanar da wani shiri na wayar da kan jama’a a Karamar Hukumar Doguwa.

Gwamnatin Jihar Kano karkashin Ofishin Ambasada Maimunat Umar Sharif, Mai Bai wa Gwamna Shawara Kan Tsaron Al’umma haɗin gwiwa da Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kano sun gudanar da wani shiri na wayar da kan jama’a a Karamar Hukumar Doguwa.

Mahalarta sun fito daga Doguwa, Tudun Wada, da sauran unguwanni da ke kewaye da wurin.

Shirin ya mayar da hankali kan ƙarfafa haɗin kai tsakanin al’umma da jami’an tsaro, inganta hanyoyin bayar da rahoton abubuwan da suka shafi tsaro, da ɗaukar matakan kariya tun kafin tashin wata matsala.

Ambasada Maimunat Umar Sharif ta jaddada cewa tsaro nauyi ne na kowa, inda ta bayyana cewa gwamnatin Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta ba tsaro muhimmanci ta hanyar tsarin tsaron al’umma da tallafawa hukumomin tsaro a matakin ƙasa da ƙasa.

A nasa jawabin, CSP M.A. Saleh, DPO na Doguwa, ya ce tsaro nauyi ne na kowa da kowa.

Sannan Ya yaba wa Gwamna Yusuf bisa jajircewarsa wajen tabbatar da zaman lafiya, ya kuma yaba da rawar da Kwamishinan ’Yan Sanda ke takawa wajen tabbatar da tsaro.

Ya Kara kira ga shugabannin al’umma, iyaye da mazauna gari da su haɗa kai da jami’an tsaro musamman a Doguwa.

Shirin ya ƙare da kira ga jama’a da su kasance masu lura, haɗin kai da aiki tare domin gina Kano ta fuskar zaman lafiya da tsaro ga kowa da kowa, inda aka tabbatar cewa haɗin gwiwar al’umma da jami’an tsaro shine mabuɗin nasara.

You may also like

Leave a Comment