Home PoliticalMaduro da matarsa na kan hanyar zuwa New York – Trump

Maduro da matarsa na kan hanyar zuwa New York – Trump

Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce Shugaban Venezuela Nicolas Maduro da matarsa na kan hanyarsu ta zuwa New York bayan dakarun Amurka sun kama su a wani hari da suka ƙaddamar.

Mista Trump ya ce an tuhumi mutanen biyu a wata kotun gunduma a New York, yayain da a yanzu za a wuce da su zuwa babban birnin jihar ta hanyar jirgi mai saukar ungulu da na ruwa.

“Sun kashe mutane da dama da Amurkawa da yawa, da mutanen ƙasarsu,” in ji Trump

A yau ne dakarun Amurka suka kama Maduro da matarsa a wani hari da ta ƙaddamar a ƙasar.

You may also like

Leave a Comment