Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya ce gwamnatinsa ba za ta taba nuna Jinkai ga ‘Yan ta’adda da ‘Yan Bindiga da masu garkuwa da mutane da kuma masu daukar nauyinsu ba.
Hakanan ya bayyana Ribanya matsa lamba ga masu aikata laifuka wanda ya ce duk ya na daga cikin matakan Sauya fasalin tsaron Kasar nan da gwamnati ta ke dauka.
Tinubu ya bayyana hakanne ayayin gabatar da kudurin kasafin kudi na shekarar 2026 na naira tiriliyan Hamsin da takwas da biliyan dari da tamanin, ga zaman hadin guiwa a tsakanin majalisar Dattawa da majalisar Wakilai ta tarayya a Abuja.
Tun kafin hakan sai da majalisar zartaswa ta kasa ta amince da daftarin kasafin kudi ayayin wani taron gaggawa da mataimakin shugaban Kasa Kashim Shettima ya Jagoranta.
A kasafin kudin, shugaban Kasa Bola Tinubu ya ware naira tiriliyan Biyar da Biliyan dari hudu da daya domin bangaren tsaro wanda shi ne kaso mafi tsoka a Kunshin kasafin kudin na shekarar 2026.
Wannan dai shi ne karo na uku a jere da bangaren tsaro Ya ke samun fifiko a kasafin Kudi tun bayan da gwamnatin ta fara gabatar da kasafin kudi ga majalisa a cikin watan Nuwamba na shekarar 2023.