Home NewsƳan Houthi da gwamnati sun amince su yi musayar fursunoni

Ƴan Houthi da gwamnati sun amince su yi musayar fursunoni

‘Yan tawayen Houthi a Yemen da gwamnatin da kasashen waje ke marawa baya sun cimma yarjejeniyar musayar fursunoni 3000 a tsakaninsu.

Wakilai daga dukkan bangarorin biyu sun tabbatar da cimma matsayar da ke xuwa bayan kusan makonni biyu da tattaunawa tsakaninsu da kasar Oman ta jagoranta.

Wakilin BBC ya ce idan hakan ta tabba wannan zai zamo musayar fursunoni mafi girma tun bayan barkewar yaki a Yemen sama da shekaru 10 da suka gabata.

Wani mai shiga tsakani a bangaren Houthi ya ce gwamnati za ta sako mambobinsu 1700, inda su kuma za su yi musayarsu da fursunonin bangaren gwamnati 1200.

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman a Yemen Hans Grundberg, ya ce su na fatan wannan zai bude wata hanya da fursunoni da iyalansu za su masu saukin wahalar da suke ciki.

You may also like

Leave a Comment