Gwamnatin Jihar Kano ta Jaddada kudirinta ganin editocin kungiyar ‘yan jarida masu yada labarai ta Kafar Internet sun shiga cikin Kungiyar editocin ta kasa domin Kara samun kwarewa da kuma kiyaye ka’aidojin aikin jarida.
Kwamishinan ma’aikatar yada Labarai da harkokin cikin gida na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya bayyana hakan a jawabin rufe horon bita na Kwanaki biyu da Gwamnatin kano ta Shiryawa ‘yan kungiyar
a Dutse, babban birnin jihar Jigawa.
Kwamared Ibrahim Waiya ya ce gwamnatin Kano gwamnati ce Wadda ta mayar da hankali wajen taimakawa harkar jarida da ‘yan jarida kasancewar su abokan tafiya wajen tabbatar da cigaban a’lumma a harkar mulkin dimokaradiyya.
kwamishinan ya ja hankalin mahalarta bitar da su yin amfani da abin da suka koya yayin bitar musamman amfani Da cigaban gasar fasahar zamani kamar AI da sauran tsarin sadarwa na zamani.
A jawabinsa bayan kammala horon bitar, Shugaban Kungiyar masu yada Labarai ta kafar Intanet Kwamared Abubakar Dangambo, ya godewa gwamnatin Jihar Kano karkashin Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf bisa daukar nauyin bitar da kuma Kwamishinan yada Labarai da harkokin cikin gida na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya bisa hidimar da suka yi wajen samun nasarar horon.
Kungiyar ta karrama Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf da Kwamishinan yada Labarai da lambar yabo bisa namijin kokari wajen kafuwar kungiyar cikin nasara a Jihar Kano.
Wasu daga cikin mahalarta bitar sun Bayyana yadda suka Karu da makaloli da kasidun da kwararrun masana a fannin yada labarai daga jami’o’i da kwararrun ‘yan jarida suka gabatar akan hanyoyin inganta aikin yada labarai ta Intanet.
Kano live 24 tarawaito cewa mahalarta taron sun karbi shedar halartar bitar, Wanda ya wakana babban birnin Dutsen Jihar Jigawa.