427
Duk da cewa akwai sauran lokaci kafin zaɓen shekarar 2027, za a iya cewa harkokin siyasa sun fara zafi a Najeriya, musamman a wasu jihohin ƙasar da suka yi fice wajen siyasa mai zafi.
A dokokin kundin hukumar zaɓen ƙasar ta INEC, har yanzu ba a fitar da jadawalin zaben 2027 ba, balle a san lokacin fara siyasa gadan-gadan.
To amma tun daga shekarar da ta gabata ne siyasa ta ɗauki zafi a wasu jihohin Najeriya, inda ƴan siyasa suka riƙa sauya sheƙa, a wasu wuraren aka fuskanci hargitsi a wasu jihohi kuma ake ta musayar yawu.
bayan dogon nazari kan jihohin Najeriya da siyasarsu ke daukan hankali gabanin zaɓen na 2027.