418
Kasashen duniya 14 da suka haɗa da Faransa da Birtaniya da Jamus da kuma Japan sun yi alawadai da amincewar da gwamnatin Isra’ila ta yi na gina sabbin matsugunan Yahudawa a yankin Gabar Yamma da Kogin Jordan.
Sanarwar ƙasashen ta hadin guiwa ta yi kira ga Isra’ila ta janye matakin.
Ƙasashen sun ce masu cewa ya saɓa wa dokar ƙasa da ƙasa kuma zai ƙara rura wutar rikici da rashin zaman lafiya a yankin.
Gwamnatin Isra’ila ta ce an amince da matakin ne domin hana samar da kasar Falasdinu.