159
Wata sanarwa da mai magana da yawun burget na shida a jihar, Umar Muhammad ya fitar, ya ce sun kai samamen ne a ranar Litinin bayan samun bayanan sirri na yadda masu garkuwan ke gudanar da ayyukansu a ƙauyen Sangai da ke karamar hukumar Karim Lamido na jihar.
Ya ce sun fatattaki waɗanda ake zargin zuwa kan iyakar Taraba da jihar Filato, inda suka tsere suka bar mutum uku da suka kama.
Rundunar sojin ta ce yanzu haka mutanen na wurinsu kuma suna samun kulawa daga bisani za a miƙa su ga ƴan uwansu.