Home NewsDarakta a Hukumar Shari’a Ya yi Karar JSC a Kotu, Yana Neman Diyyar Naira Miliyan 100 Kan Ritayar Dole

Darakta a Hukumar Shari’a Ya yi Karar JSC a Kotu, Yana Neman Diyyar Naira Miliyan 100 Kan Ritayar Dole

Wani Darakta mai riƙon mukamin Sashen Hulɗa da ‘Yan Jaridu da Kididdiga a Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Shari’a ta Jihar Kano, Muzambilu Ado, ya shigar da ƙara a Kotun Ƙwadago ta Ƙasa, inda yake neman a biya shi diyyar Naira miliyan 100 tare da soke umarnin ritayar dole da Hukumar Kula da Da’ar Ma’aikatan Shari’a ta Jihar Kano ta yi masa.

Hukumar ta JSC ta ce ta ɗauki matakin ne bayan wani kwamitin tantancewa ya gano abin da ta bayyana a matsayin rashin daidaito da sauya bayanai a takardun karatun Ado, tare da zarginsa da amfani da takardun shaidar karatu na bogi domin samun aiki a Hukumar Shari’ar Jihar Kano.

Sai dai Ado ya musanta matakin, yana mai cewa an bata masa suna tare da lalata masa martaba da kuma aikin da ya shafe shekaru yana ginawa.

A wata sanarwa da mai magana da yawun Hukumar JSC, Baba Jibo Ibrahim, ya fitar mai ɗauke da kwanan watan 6 ga Yuli, 2026, hukumar ta ce ta umarci Ado da ya yi ritayar dole nan take bayan bincike ya gano manyan matsaloli a takardunsa, ciki har da zargin sauya bayanai da kuma samun shiga Makarantar Koyon Aikin Lauya ta Ƙasa ba tare da amincewar Hukumar ba.

You may also like

Leave a Comment