Gwamnan Jahar Kaduna Sanata Uba Sani ya
karbi Bakuncin Sabon Ministan Tsaron Nigeria
Janar christopher Musa a wata ziyarar aiki da ya
kai Jahar inda ya yi Alkawarin hada giuwa domin
kyautata tsaro a fadin Jahar.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X
Gwamnan Jahar Kaduna Uba Sani ya ce ya yi
matukar farinciki da ya karbi bakuncin ministan
tsaron Nigeria Janar Christopher Musa mai
ritaya inda ya taya shi murnar nadin da
shugaban Kasa ya yi masa tare da Alkawarin
samun goyon baya daga jahar Kaduna.
Ya kara da cewa sun tattauna akan batutuwa da
su ka shafi kyautatuwar tsaro a jahar Kaduna da
kuma yadda ake tattara bayanan sirri a jahar.
Gwamna Uba Sani ya ce tabbatar da tsaro
al’ummar jahar Kaduna shi ne babban abin da ya
fi baiwa fifiko, a donhaka ya ce za su kyautata
hadin guiwa da hukumomin gwamnatin tarayya
wajen tabbatar da dorewar zaman lafiya a jahar
kaduna.