Hukumar kula da ƴan gudun hijira ta Majalisar ɗinkin duniya ta ce aƙalla ƴan gudun hijira dubu casa’in ne ke tserewa daga Kudancin Kivu a Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo zuwa Burundi saboda ƙaruwar tashin hankali.
Mutanen da suka rasa matsugunansu na fuskantar mawuyacin hali a sansanin ƴan gudun hijira, kuma ba sa samun isassun abinci da ruwa.
Kungiyar agaji ta Doctors without Borders ta bayyana damuwarta kan yadda kiwon lafiya ke taɓarɓarewa da kuma matsalar agaji.
Kungiyar ta ce ta na kula da aƙalla mutum 200 a kullun, tun bayan da ƴan gudun hijirar suka soma isa Burundi makonni biyu da suka gabata.
Kusan rabin mutanen da suka rasa muhallansu yara ne ƴan kasa da shekara 18, da dama kuma mata ne ciki har da masu juna biyu waɗanda rahotanni ke cewa sun kwashe kwanaki ba su ci abinci ba.