Home NewsHukumar kula da sufurin Jiragen kasa ta Najeriya ta ce farfaɗo da jigilar kaya ta titin jirgin kasa zai taka muhimmiyar rawa wajen sauya fasalin tattalin arzikin ƙasar nan.

Hukumar kula da sufurin Jiragen kasa ta Najeriya ta ce farfaɗo da jigilar kaya ta titin jirgin kasa zai taka muhimmiyar rawa wajen sauya fasalin tattalin arzikin ƙasar nan.

Shugaban hukumar Injiniya Fidet Okhiria Okhiria wanda ya shaida hakan ya ce dawo da wannan tsari zai rage yawan dogaro da manyan motoci a kan titunan ƙasa, lamarin da zai taimaka wajen rage haɗurran ababen hawa,da kuma tsadar gyaran su.

A cewarsa, jigilar kaya ta hanyar jirgin kasa hanya ce mafi araha,sannan mai sauri kuma mai aminci, wadda za ta taimaka wa ’yan kasuwa, da manoma da masana’antu wajen rage kuɗin sufuri, tare da ƙara ribar kasuwanci.

Shugaban ya ƙara da cewa farfaɗowar harkar titin jirgin kasa zai ƙarfafa ayyukan noma da masana’antu, ya sauƙaƙa fitar da kayayyaki zuwa tashoshin jiragen ruwa, sannan ya taimaka wajen ƙara kuɗaɗen shiga ga gwamnati.

Ya bayyana cewa Hukumarsa na aiki tare da kamfanoni masu zaman kansu da masu zuba jari domin tabbatar da dorewar jigilar kaya ta dogo, tare da faɗaɗa hanyoyin dogo zuwa manyan cibiyoyin kasuwanci da masana’antu a faɗin Najeriya.

You may also like

Leave a Comment