Amurka ta kai wasu jerin hare-hare a kan kungiyar IS a kasar Syria, a matsayin martanin kisan sojojinta biyu.

Rundunar sojin Amurkar ta ce, an kai harin kan wurare sama da 70, da jiragen sama na yaki, da masu saukar ungulu da kuma makaman atilare.

Mouaz Moustafa babban darektan wata kungiyar kamun kafa ta Syria da ke Amurka ya ce da alamu wasu hare-haren za su biyo baya.

Ya ce, lalle za a ci gaba da ganin matakin Amurka da ma na gwamnatin Syria musamman a yankin Baadiya.

Shugaba Trump ya ce kamar yadda ya yi alkawari, Amurka na mayar da martani mai tsanani – kuma gwamnatin Syria da Ahmed al Sharaa ke jagoranta na bayar da cikakken goyon baya.

You may also like

Leave a Comment