Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da kafa wata runduna ta musamman domin yin aikin inganta tsaro a tashoshin mota da sauran muhimman wuraren jama’a a fadin jihar.

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da kafa wata runduna ta musamman domin yin aikin inganta tsaro a tashoshin mota da sauran muhimman wuraren jama’a a fadin jihar.

Wannan sanarwa ta fito ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Lahadi.

A cewar sanarwar, matakin na nuna ƙwarin gwiwar gwamnan wajen dakile masu aikata laifuka daga amfani da Kano a matsayin mafaka, musamman a manyan wuraren shiga da fita cikin birnin.

An bayyana tashoshin mota a matsayin wuraren da ke da hatsarin gaske ta fuskar tsaro saboda yawan cunkoson jama’a da kuma sabbin matsalolin tsaro, ciki har da kama wasu da ake zargin masu laifi ne a tashar motar Kofar Ruwa.

Rundunar aikin za ta mayar da hankali ne kan sa ido sosai da tattara bayanan sirri da gudanar da ayyukan tsaro tare a tashoshin mota da sauran wuraren da ke da karancin tsaro.

Gwamna Yusuf ya ce wannan mataki wata hanyar ba da kariya ne domin dakile barazanar tsaro tun kafin ta tsananta.

Ya ƙara da cewa hakan zai inganta haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro tare da dawo da kwarin gwiwar al’umma.

Gwamnan ya kuma jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci aikata laifi ba, tare da tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da bai wa hukumomin tsaro cikakken goyon baya domin kare rayuka da dukiyoyin jama’ar jihar Kano.

You may also like

Leave a Comment