Home NewsShugaban Amurka Donald Trump ya ce, za a mayar wa ƙungiyar IS mummunan martani, bayan da wani harin kwanton-ɓauna da aka kai a tsakiyar Syria, ya hallaka sojojin Amurka biyu da wani tafinta.

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce, za a mayar wa ƙungiyar IS mummunan martani, bayan da wani harin kwanton-ɓauna da aka kai a tsakiyar Syria, ya hallaka sojojin Amurka biyu da wani tafinta.

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce, za a
mayar wa ƙungiyar IS mummunan martani,
bayan da wani harin kwanton-ɓauna da aka kai a
tsakiyar Syria, ya hallaka sojojin Amurka biyu da
wani tafinta.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a yankin
Palmyra inda ake sintri na hadin gwiwa tsakanin
sojin Syria da na Amurka

Sojojin na cikin tawagar hadin gwiwa ta tsakanin
Syria da Amurka da ke yaki da ta’addanci –
lokacin da suke sintiri a kusa da birnin Palmyra.

Ita ma gwamnatin Syria ta fitar da sanarwa inda
ta yi Alla-wadai da harin.

Jami’ai sun ce an jikkata wasu jami’an tsaro uku
a harin, inda aka kashe ɗan bindigar.

Ana ci gaba da ɓoye sunayen waɗanda aka
kashe na tsawon sa’o’i 24 har sai an sanar da
‘ƴan uwansu.

A baya-bayan nan Syria ta shiga cikin ƙawancen
ƙasa da ƙasa don yaƙar ƙungiyar IS kuma ta yi
alƙawarin haɗa kai da Amurka.

You may also like

Leave a Comment