Sheikh Isa Pantami Ya Yi Magana kan Rade Radin Cewa zai Auri Aisha Buhari
10 Jan 2026
Ibrahim Yusuf wanda ya yi bita Muhammad Malumfashi 3 – tsawon mintuna Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami ya fito karara ya musanta rade-radin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa yana shirin auren Aisha Buhari Tsohon minista, Pantami ya jaddada cewa marigayi Muhammadu Buhari uba ne a gare su, yayin da matarsa Aisha Buhari take a matsayin uwa Wasu jama’a sun yi martani karkashin sakonsa, suna bayyana cewa jita-jitar ba ta da tushe kuma gaskiya ta riga ta bayyana bayan ya yi bayani
Tsohon ministan sadarwa, Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami, ya yi karin haske kan rade-radin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke alakanta shi da shirin auren uwargidan marigayi Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari. Pantami, wanda ya yi aiki a gwamnatin marigayi Buhari, ya bayyana rade-radin a matsayin kirkirarren labari mara tushe, yana mai cewa abin ya ba shi mamaki matuka.
Pantami ya wallafa sakon karyata shirin auren ne a Facebook bayan jita-jitar ta bazu sosai a kafafen sada zumunta, lamarin da ya haifar da muhawara da martani daga jama’a da dama a fadin kasa. –