Home NewsSomaliya da Masar za su hana amincewa da Somaliland

Somaliya da Masar za su hana amincewa da Somaliland

Somaliya da Masar sun amince su hana Somaliland samun amincewa a matakin ƙasa da ƙasa, bayan Isra’ila ta bayyana a watan Disambar 2025 cewa ta amince da ita a matsayin ƙasa mai cikakken ‘yancin kai.

Wannan yarjejeniya ta biyo bayan tattaunawar da ministocin harkokin wajen Somaliya da Masar, Abdisalam Abdi Ali da Badr Abdelatty, suka yi a taron ƙungiyar haɗin kan ƙasashen musulmai (OIC) da aka gudanar a Jeddah ranar 10 ga Janairu.

Ministocin biyu sun yi watsi da matakin Isra’ila, suna mai cewa matakin na ƙalubalantar iyakokin Somaliya da duniya ta amince da su.

Kungiyar OIC, wadda ta ƙunshi ƙasashe 57 masu rinjayen Musulmi, ta gudanar da taron ne domin tattauna matakin Isra’ila da yiwuwar ɗaukar matsaya tare.

Somaliland ta ayyana namen ƴancin kai daga Somaliya tun 1991, kuma Isra’ila ce ƙasa ta farko kuma kaɗai daga cikin mambobin Majalisar Ɗinkin Duniya da ta amince da ita a hukumance a watan Disambar da ya gabata.

You may also like

Leave a Comment