Home NewsAkwai Matsala” – Al’ummar Kabo Ba Zamu Yi APC Ba, Matukar Ba A Gyara Ba.

Akwai Matsala” – Al’ummar Kabo Ba Zamu Yi APC Ba, Matukar Ba A Gyara Ba.

Ƙungiyar Daliban Ƙaramar Hukumar Kabo (Kabo Local Government Students Association – KALSA) ta bayyana cewa akwai buƙatar gyara a fannin ilimi a ƙaramar hukumar, tare da kira ga Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da ya umarci a gudanar da cikakken bincike kan yadda ake kashe kuɗaɗen gwamnati da aka ware domin ilimi a ƙaramar hukumar.

Ɗaya daga cikin shugabannin ƙungiyar, Comrade Malam Sani Kabo, ya ce tun daga shekarar 2023 suke fafutukar neman tallafi ga ɗaliban Kabo da ke karatu a manyan makarantu, musamman marayu da kuma ‘ya’yan marasa ƙarfi, domin su samu damar ci gaba da karatunsu.

A cewarsa, duk da ƙoƙarin da suke yi, har yanzu ana fuskantar ƙalubale wajen tallafa wa ɗalibai, lamarin da ya sa suka nemi a binciki yadda ake gudanar da harkokin ilimi da kuma kashe kuɗaɗen gwamnati a ƙaramar hukumar.

A ƙarshe, ƙungiyar ta yi kira ga Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya ɗauki matakin da ya dace kan lamarin, tana mai gargadin cewa rashin ɗaukar mataki na iya yin tasiri a zaɓe mai zuwa.

You may also like

Leave a Comment