44
Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya sauke Kwamishinan Kasuwanci, Masana’antu da Zuba Jari, Mohammed Salis Gamawa, da Kwamishinan Wutar Lantarki, Kimiyya da Fasaha, Dakta Mohammed Lawal Rimin Zayam.
Mai magana da yawun gwamnan, Mukhtar Gidado, ya ce matakin ya fara aiki nan take, kuma an tura sunayen waɗanda za su maye gurbinsu zuwa Majalisar Dokokin Jihar domin tantancewa.
Haka kuma, gwamnan ya amince da murabus ɗin tsohon Kwamishinan Raya Karkara da Ayyuka na Musamman, Faruk Mustapha, tare da gode wa dukkan waɗanda suka bar mukamansu bisa gudummawar da suka bayar ga ci gaban jihar.