Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ICPC ta ƙi amincewa da buƙatar da attajirin Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ya gabatar na janye ƙorafin da ya shigar kan Engr. Farouk Ahmed, tsohon babban daraktan hukumar kula da harkokin man fetur ta Ƙasa NMDPRA.
ICPC ta bayyana cewa ta riga ta fara bincike kan zarge-zargen da aka yi akansa kuma za a ci gaba da gudanar da shi bisa tanadin dokokin da suka kafa hukumar, ko da mai ƙorafin ya janye ƙarar.
Wata sanarwa daga kakakin ICPC, John Odey, ta tabbatar da karɓar wasiƙa daga lauyoyin Dangote ɗauke da kwanan wata 5 ga Janairun 2026, mai taken “Sanarwar Janye Ƙorafi kan Injiniya Farouk Ahmed, tsohon ACE/CEO na NMDPRA.”
Sanarwar ta kuma nuna cewa wasiƙar ta yi nuni da cewa wata hukumar tsaro daban ce ta karɓi batun.
Sai dai ICPC ta jaddada cewa hakan ba zai hana ko dakatar da binciken da take gudanarwa ba.
Hukumar ta nanata cewa tana da cikakken ikon doka da alhakin ci gaba da bincike kan duk wani zargi da ya shafi cin hanci da rashawa, domin kare muradun jama’a da tabbatar da gaskiya da adalci.