Home NewsDuk jami’in gwamnatin Kano da aka matsa masa, ya koma APC – Kwankwaso

Duk jami’in gwamnatin Kano da aka matsa masa, ya koma APC – Kwankwaso

Jagoran jam’iyyar NNPP kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya shawarci magoya bayansa da ke aiki a gwamnatin jihar Kano da su sanya hannu kan duk wata takarda da ke buƙatar amincewar su ta sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC.

Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da siyasar Kano ta ɗauki ɗumi, musamman bayan bayanai sun fito kan cewa gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, na shirin sauya sheƙa daga jam’iyyar NNPP zuwa APC.

A wani bidiyo da ya wallafa a shafin Facebook, Kwankwaso ya yi zargin cewa gwamnatin Kano na matsa wa shugabannin ƙananan hukumomi da kansiloli da masu riƙe da muƙamai su bayyana aniyarsu ta sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC.

Ya ce: “Gwamnati ta fito da wani tsari na takura wa ciyamomi da kansiloli da sakatarori da sauran masu riƙe da muƙami wajen rubuta sunansu don nuna ko suna goyon bayan Kwankwasiyya ko Gandujiyya.”

Kwankwaso ya bayyana rashin gamsuwarsa da abin da ke faruwa, amma ya jaddada cewa talakawa sun nuna goyon baya ga jam’iyyarsa a baya duk da waɗannan ƙalubale.

Ya ce umarnin da ya bai wa mabiyansa na sanya hannu a irin waɗannan takardun, na da nufin sauƙaƙa musu nauyi da kare su daga matsin lamba, domin kada su shiga mawuyacin hali a siyasa.

You may also like

Leave a Comment