Home NewsAna fargabar wasu ƴan bindiga sun yi awon-gaba da mutum 32 ciki har da ƙananan yara tare da kashe mutum 1 a wani hari da suka kai garin Kadagen Kauru da ke ƙaramar hukumar Kauru ta jihar Kaduna.

Ana fargabar wasu ƴan bindiga sun yi awon-gaba da mutum 32 ciki har da ƙananan yara tare da kashe mutum 1 a wani hari da suka kai garin Kadagen Kauru da ke ƙaramar hukumar Kauru ta jihar Kaduna.

Harin na zuwa ne bayan wani makamancinsa da ƴanbindiga suka kai a watan da ya gabata, inda ake zargin sun sace mutum 85 a garin Kabari da ke makwabtaka da garin na Kadagen Kauru, bayan ga jerin hare-hare da suka kai wasu daga cikin ƙauyukan yankin.

Bayanai sun tabbatar da cewa ana ci gaba da alhinin sace mutanen da ƴanbindigan suka yi a ranar Litinin a garin.

You may also like

Leave a Comment