Home NewsRundunar Sojin Saman Nigeria ta ce Sojoji kadai ba za su iya samar da zaman lafiya mai dorewa ba a kasar nan har sai an yi amfani da diflomasiyya da kuma hadin guiwa wajen magance kalubalen tsaron kasar nan.

Rundunar Sojin Saman Nigeria ta ce Sojoji kadai ba za su iya samar da zaman lafiya mai dorewa ba a kasar nan har sai an yi amfani da diflomasiyya da kuma hadin guiwa wajen magance kalubalen tsaron kasar nan.

Babban Hafsan Rundunar Sojin Saman
Nigeria Air Marshal Sunday Aneke ya
bayyana hakan a sakon da ya aike ayayin
taron majalisar Jami’an Diflomasiyya na
kasa da kasa da ya gudana a Abuja.

A cewarsa diflomasiyya shi ne babban Ikon
da kasa ta ke amfani da shi wajen cimma
biyan bukata ba tare da amfani da karfjn soji
ba musamman a lokacin da ake fama da
barazanar tsaro a Nigeria da kuma shiyyar
Afirka ta yamma.

Babban Hafsan ya ce Rundunar Sojin
Saman Nigeria ta na da manufa irin ta
Kungiyar Jami’an diflomasiyya na kasa da
kasa wajen samar da zaman lafiya ta amfani
da hadin kan kasashen duniya inda ya ce
karfafa hadin guiwa a tsakanin Rundunar
Sojin saman Nigeria da kuma Kungiyar
Jami’an Diflomasiyya na kasa da kasa zai
taimaka wajen wayar da kai dangane da
harkokin tsaro a Nigeria da kuma karfafa
hadin guiwa a tsakanin kasashen duniya.

You may also like

Leave a Comment