Home NewsEthiopia za ta gina sabon baban filin jirgin sama

Ethiopia za ta gina sabon baban filin jirgin sama

Firministan Ethiopia, Abiy Ahmed ya ƙaddamar da aikin ginin wani sabon babban filin jirgin sama mafi girma a tarihin Afirka

Babban filin jirgin saman na Bishoftu za a gina shi tazarar kilomita 45 daga Addis Ababa, babban birnin ƙasar.

Idan an kammala aikin zai zama ƙari kan filin jirgin Addis Ababa da ake da shi yanzu.

Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Mista Abiy ya ce sabon filin jirgin zai mayar da ƙasar zama ɗaya daga cikin manyan ƙasashen masu ƙarfin sufurin jiragen sama.

Ana sa ran kammala aikin gina sabon filin jirgin nan da shekarar 2030.

You may also like

Leave a Comment