Home NewsSojoji sun dakile harin ISWAP a borno inda su ka hallaka ‘yan ta’adda yayin da suke tserewa

Sojoji sun dakile harin ISWAP a borno inda su ka hallaka ‘yan ta’adda yayin da suke tserewa

Sojoji sun dakile harin ISWAP a borno inda su ka hallaka ‘yan ta’adda yayin da suke tserewa

Dakarun Sojin Najeriya sun dakile harin ISWAP a Azir, Damboa, Borno, inda suka hallaka da dama daga ‘yan ta’addan kuma suka tilasta wasu guduwa kamar yadda shafin Zagazola Makama ya rawaito.

Bangaren Sojin Sama (NAF) ya bayar da tallafin kai hari daga sama, inda jiragen sama suka bibiyi ‘yan ta’addan da suka tsere, suka kuma kai musu hari daidai wuraren da suke.

A yayin artabun, wasu motocin sojoji sun kone sakamakon harbin RPG, amma sojoji sun ci gaba da rike yankin.

An kwato makamai da alburusai da dama daga wuraren da ‘yan ta’addan suka bari, ciki har da bama-baman gida, da harsashin bindiga.

Majiyoyi sun ce aikin ya cimma nasara, inda an raunana karfin ‘yan ta’addan na sake kai hari a yankin, kuma hare-haren sun sa su asara mai yawa.

You may also like

Leave a Comment