Home NewsDalibai da ma’aikatan Kwalejin fasaha ta Potiskum, a Jihar Yobe makarantar da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya kammala a matsayin ɗalibi sun nuna damuwa kan halin da makarantar ta samu kanta inda gine-gine da kayan aiki suka lalace sosai.

Dalibai da ma’aikatan Kwalejin fasaha ta Potiskum, a Jihar Yobe makarantar da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya kammala a matsayin ɗalibi sun nuna damuwa kan halin da makarantar ta samu kanta inda gine-gine da kayan aiki suka lalace sosai.

Kwalejin ake kallo a matsayin alfahari a fannin ilimin fasaha a arewa‑maso‑gabashin ƙasar nan yanzu tana fuskantar matsaloli da dama, ciki har da rusassun gine-gine,da tagogi da suka karye,da rufin da ke zubawa,da kayan aiki marasa amfani.

Wani ɗalibi ya shaida wa manema labarai cewa suna jin tsoron amincin rayuwarsu a cikin ajujuwa saboda ƙarar rufin yayin iska da ruwan sama a duk lokacin Damuna.

Haka zalika, ɗalibai masu nazarin fasaha sun yi korafi cewa rashin kayan aikin zamani da bitoci masu inganci yana rage musu damar samun ƙwarewa yadda ya kamata a fannin da suke karatu.

Wasu ɗaliban sun nuna damuwa kan matsalar tsafta da rashin tsaro a dakunan su, inda suka ce duhu da ƙarancin fitilu suna sanya rashin jin daɗi da tsoro musamman a daren dare.

Iyaye da shugabannin al’umma suma sun nuna takaici kan lamarin, suna mai cewa yana da wuya a yarda irin wannan hali ya faru a makarantar da ta samar da shugabanni da dama, suna kira ga gwamnati da ta hanzarta gyara.

Jami’in gudanarwa na makarantar, wanda ya nemi a boye sunansa, yace matsalolin sun yi yawa kuma kudin da ake basu na gudanawarwa baya isarsu.

You may also like

Leave a Comment