A cewar rahotanni kayayyakin da kuma magungunan marassa Inganci an kwato su ne daga jahohin Nassarawa da Kogi da Benue da Niger da kuma Jahar Plateau inda kuma aka lalata su a sashen Kona gurbatattun kayayyaki da ke a Unguwar Rere a birnin lafiya na jahar Nassarawa.
Shugabar Hukumar NAFDAC Farfesa Mojisola Adeyeye ta bayyana cewa gurbatattun kayyayyakin da kuma magungunan, hukumar NAFDAC ta kwace su ne ayayin gudanar da aiyukanta na sanya ido tare da duba kayayyakin abinci da magunguna da ba su da Inganci a Kasuwanni.
Shugabar hukumar NAFDAC wadda ta sami wakilcin Babban Daraktan da ke kula da Shiyyar Arewa ta tsakiya Kenneth Azikiwe ta ce gangamin aikin na da manufar hana gurbatattun kayan abinci da magunguna shiga cikin kasuwanni tare da haifar da illa ga al’umma.
A cewarta daga cikin kayayyakin da aka lalata akwai gurbatattun magunguna da kayan gwaje-gwaje na likitoci na bogi da aka kera da kayan ciye-ciye irinsu Biskit da Cingam masu hadari ga koshin lafiya da sabulai da kayan wanki da kuma Sinadarai masu hadari ga Koshin lafiya.
Shugabar hukumar ta NAFDAC ta ba da tabbacin cewa za ta cigaba da tabbatar da cewa Ingantattun kayan abinci da magunguna ne kadai su ke shiga cikin kasuwannin Nigeria domin amfanin al’umma.