Home NewsShugaban Majalisar Wakilai ta kasa Tajudden Abbas ya yi Alkawarin cewa majalisar za ta dauki nauyin biyan kudaden wata-wata na kulawa da koshin lafiyar masu Bukata ta musamman a karkashin shirin kulawa da Koshin lafiya da ke aiki da Kirkirarriyar Fasaha na tsahon shekaru Biyar anan gaba.

Shugaban Majalisar Wakilai ta kasa Tajudden Abbas ya yi Alkawarin cewa majalisar za ta dauki nauyin biyan kudaden wata-wata na kulawa da koshin lafiyar masu Bukata ta musamman a karkashin shirin kulawa da Koshin lafiya da ke aiki da Kirkirarriyar Fasaha na tsahon shekaru Biyar anan gaba.

Tajudden ya yi Alkawarinne ayayin
kaddamar da shirin kulawa da koshin lafiyar
masu Bukata ta musamman a Nigeria wada
ya gudana a Abuja.
Shugaban Majalisar Wakilan ta Nigeria
Tajudden Abbas wanda mataimakin
shugabqn kwamitin Makamashi na Majalisa
Joshua Gana ya wakilta ya ce a ko ina a
fadin duniya Kirkirarriyar fasaha ta na haifar
da sauyi a fannin kulawa da koshin lafiya.
Ya ce ta amfani da manhajar mai suna
(KOYO) majinyata a kasar nan za su iya cin
gajiyar samun kulawar gogaggun likitoci ta
hanyar amfani da shawarwarin kirkirarriyar
Fasaha a fannin kiwon lafiya daga bangarori
daban-daban.
Hakanan Shugaban majalisar wakilai ta kasa
ya yi Alkawarin samun goyon bayan
majalisar ta fuskar dokoki domin samun
dorewar shirin.

You may also like

Leave a Comment