Home BusinessMutum 8 sun mutu a hare-haren sojojin Amurka kan jiragen da ake zargi da safarar ƙwayoyi

Mutum 8 sun mutu a hare-haren sojojin Amurka kan jiragen da ake zargi da safarar ƙwayoyi

Sojojin Amurka sun ce sun kai hare-hare kan jiragen ruwa uku da ake zargi da safarar ƙwayoyi a Tekun Pasifik, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum takwas.

Rundunar sojin kudancin Amurka ta wallafa faifan bidiyon hare-haren a shafukan sada zumunta, inda ta ce jiragen na tafiya ne ta hanyoyin da aka san ana safarar miyagun ƙwayoyi, kuma suna cikin ayyukan safarar kwayoyi.

A cewar sojojin, sama da jiragen ruwa 20 a Tekun Pasifik da na Caribbean aka kai wa hare-hare a ‘yan watannin nan, inda aƙalla mutum 90 suka rasa rayukansu.

Wannan wani ɓangare ne na tsaurara matakan da shugaba Donald Trump ke ɗauka kan ƙungiyoyin da yake zargi da safarar kwayoyi zuwa yankin.

Sai dai wasu masana sun ce waɗannan hare-hare na iya saɓawa dokokin yaƙi na kasa da kasa.

Harin farko da aka kai a ranar 2 ga Satumba ya jawo ce-ce-ku-ce musamman, domin an ce an kai hari sau biyu inda waɗanda suka tsira daga harin farko aka kashe su a na biyu.

Wasu kwararrun masana shari’a sun shaida wa BBC Verify cewa harin na biyu da sojojin Amurka suka kai kan wani jirgin ruwa mai safarar ƙwayoyi da ake zargin na Venezuela ne, mai yiyuwa ya saɓa doka, kuma ana iya ɗaukarsa a matsayin kisan gilla ba tare da shari’a ba a karkashin dokar kasa da kasa.

A martaninta, Fadar White House ta ce matakan da aka ɗauka sun yi daidai da dokokin yaƙi, domin kare Amurka daga kungiyoyin safarar kwayoyi da take zargin suna kokarin “shigar da guba zuwa kasar da lalata rayukan ‘yan ƙasar.

You may also like

Leave a Comment