Home NewsRundunar ‘Yan sanda a jahar Sokoto ta kama wani Muhammad Mukhtar wanda Jagora ne na Kungiyqr Matsafa ta ‘sai Malam’ tare da wani Katon Maciji da dai sauran kayayyakin tsafe-tsafe.

Rundunar ‘Yan sanda a jahar Sokoto ta kama wani Muhammad Mukhtar wanda Jagora ne na Kungiyqr Matsafa ta ‘sai Malam’ tare da wani Katon Maciji da dai sauran kayayyakin tsafe-tsafe.

Kwamishinan ‘Yan sanda a jahar Sokoto Ahmad Musa ya bayyana hakan ayayin da ya ke gargadin matasa da su kiyayi
shiga Kungiyar ta ‘sai malam’ wadda ya bayyana a matsayin sabuwar Kungiyar Matsafa a Jahar.

A cewar Kwamishinan aiyukan Kungiyar a bayabayannan ya haifar da firgici da kuma razana ga al’ummar Jahar Sokoto.

Ya ce Simamen Rundunar na da nasaba da Kokarin da Rundunar ta ke na tabbatar da Dorewar zaman lafiya da tsaron
al’umma da kuma karya lagon dukkan wata barazanar tsaro a fadin jahar Sokoto.

You may also like

Leave a Comment