23
Sai dai ƙungiyar ta amince cewa ci gaba da bayar da tallafin man fetur ma yana da nasa nauyin kashe kuɗi da haɗurran tattalin arziki, tana mai cewa duk wani sauyi ya kamata ya daidaita dorewar tattalin arziki da adalci ga al’umma.
Sanarwar, wadda Ambasada Abdullahi Bakoji Adamu, Daraktan ƙungiyar na ƙasa ya sanya wa hannu, ta ƙara da cewa nasarar manufofin tattalin arziki ba ta tsaya ga kuɗin da gwamnati ta tara ba, sai dai yadda suka inganta rayuwar jama’a, hanyoyin samun abin dogaro da mutuncin ɗan Adam.
Ƙungiyar ta jaddada cewa ya kamata al’umma su kasance a tsakiyar dukkan manufofi da harkokin mulki.