Majalisar ministocin ƙasashen yammacin
Afrika da ke ƙarƙashin ECOWAS ta kammala
tarota karo na 95, wanda ya tattaunawa kan
harkokin tsaro da siyasa da kuma tattalin
arzikin yankin.
Ministan harkokin waje Saliyo Timothy
Kabba ne ya jagoranci taron da aka gudanar
tsakanin 10 zuwa 12 ga wannan wata a
Abuja, wanda ya nazarci ƙalubalen da
yankin ke fuskanta.
Ministocin sun tattauna game da yaɗuwar
tsattsauran ra’ayi haɗi da ƙananan makamai
a yankin Sahel, da matsalolin tsaro cikin
harda na mashigar tekun Guinea da kuma
juyin mulkin da ake samu a yankin.
A jawabinsa wajen rufe taron, Timothy
Kabba ya ce taron ya kuma yi nazari kan ci
gaban siyasa a ƙasashe mambobikin
ƙungiyar da kuma irin tasirin da suke da shi
wajen gudanar da mulkin dimukaraɗiyya,
inda ya ce Saliyo na goyon bayan ECOWAS
ta amince da kare mulki dimukaraɗiyya a
yankin baki daya.