Home NewsFiraministan Sudan Kamil Idris a birnin NewYork, zai gana da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres da nufin kawoƙarshen rikicin ƙasar da kuma samun tallafin jinkai a ƙasar da yakin basasa ya jefa jama’a cikinmayuwacin hali.

Firaministan Sudan Kamil Idris a birnin NewYork, zai gana da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres da nufin kawoƙarshen rikicin ƙasar da kuma samun tallafin jinkai a ƙasar da yakin basasa ya jefa jama’a cikinmayuwacin hali.

Tsawon shekaru ƙasashen duniya na kokarin gani an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin sojojin Sudan da kuma rundunar sa kai ta RSF,wanda hakan ya ci tura.

Ƙungiyoyi a ciki da wajen ƙasar na bayyana cewa yaƙi ma na ƙara tsananta a yankin Kordofan da ke kudancin ƙasar, wanda hakan ya haifar da fargabar kisan gilla irin wanda aka yi a lokacin da RSF ta kama El-Fasher a ƙarshen watan Oktoba, inda rahotanni da dama suka ruwaito kisan gilla da fyaɗe da kuma kwacen kayan agaji.

Antonio Guterres ya bayyana a farkon wannan watan cewa ya na shirya tattaunawa da ɓangarorin biyu na ƙasar ta Sudan.

You may also like

Leave a Comment