A daidai lokacin da ake ci gaba da muhawara kan cika shekara 60 da juyin mulkin soji na farko a Najeriya, wanda ya yi sanadiyar kifar da gwamnatin jamhuriya ta farko, wasu na ci gaba da tattaunawa kan tabon da matsalar ta haifar.
Juyin mulkin ne ya yi sanadiyar mutuwar fitattun ƴansiyasa irin su Firaministan Najeriya na wancan lokaci Abubakar Tafawa Ɓalewa da Firimiyan Arewa Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto da takwaransa na Yamma Ladoke Akintola da sauransu.
A yunƙurin juyin mulkin, wanda aka yi a ranar 15 ga watan Janairun shekarar 1966, wasu hafoshin sojin Najeriya ne suka yi yunƙurin juyin mulki, wanda shi ne na farko da aka fara samu bayan samun ƴancin kai.
Baya ga manyan ‘yan siyasa, juyin mulkin ya kuma rutsa da manyan jami’an sojin Najeriya.
Wani abu da yake ci gaba da ɗaukar hankali shi ne yadda aka binne marigayi Sardauna Sokokot a Kaduna, maimakon jiharsa ta Sokoto, kamar yadda aka binne sauran waɗanda aka kashe jihohinsu na asali.