Home NewsShugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya Kara musanta cewa mabiya addinin kirista na fuskantar kisan kare dangi a Nigeria.

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya Kara musanta cewa mabiya addinin kirista na fuskantar kisan kare dangi a Nigeria.

A cewar shugaban Kasa daga mabiya
addinin kirista zuwa mabiya addinin
musulunci babu wanda ake da burin
Kaddamarwa da kashe-kashe a Nigeria.

Tinubu ya ce rashin tsaron da ke addabar
Kasar nan ya samo Asali ta fuskar tarihi da
tattalin arziki da kuma wasu laifuka da ake
aikatawa amaimakon danganta hakan da
addini a cewarsa.

Shugaban Kasa ya bayyana hakanne ayayin
bude taron Kungiyar musulmai ta Nasrullahi
Fatih karo na Takwas wanda ya ke gudana a
duk bayan shekaru biyu a Abuja.

Tinubu wanda ya sami wakilci Minjstan
shari’ah Lateef Fagbemi ya ce Nigeria ta na
fama da aiyukan ta’addanci da ke da nasaba
da laifuka da ake tafkawa da kuma
tsattsauran ra’ayin addini.

You may also like

Leave a Comment