Sojojin Turai na shiga yankin Greenland don samar da kariya
Sojojin wasu kasashen Turai sun fara ba da kariya ga yankin Greenland mai yanci, bayan karuwar barazanar da ke fitowa daga Amurka kan neman shiga yankin da karfin tuwo. Denmark dai ta tsaya domin kare yankin.
Dakarun sojin kasashen Turai da dama, ciki har da na Jamus da Faransa, na ci gaba da dannawa zuwa tsibirin Greenland mai ‘yancin kai domin nuna goyon baya ga kasar Denmark.
Wannan na zuwa ne bayan da tattaunawar da aka yi tsakanin Amurka da wakilan Denmark da Greenland ta gaza cimma matsaya kan makomar wannan tsibiri na yankin Arctic mai dausayin kankara.
Fadar White House ta nanata cewa mataki na gaba yanzu shi ne tattaunawar fasaha kan yarjejeniyar da za ta bai wa Amurka damar sayen yankin na Greenland.
Sai dai ministan harkokin wajen Denmark, Lars Løkke Rasmussen, ya musanta wannan ikirari, inda ya ce an kafa tawaga ta musamman da za ta tattauna yadda za a warware sabanin da ke tsakanin kasashen