Shugaban ƙasar Masar, Abdel-Fattah El-Sissi, ya sake jaddada buƙatar da ke akwai na yin sauye-sauyen tsari a Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya domin bai wa Afirka muhimmanci da kuma bata damar takarawa a yanke manyan hukunce-hukunce a duniya.
El-Sissi ya bayyana hakan ne a yayin taron haɗin gwiwar Rasha da Afirka da aka gudanar a Cairo, wanda Ministan Harkokin Wajen Rasha, Sergey Lavrov, ya halarta tare da ministoci daga ƙasashen Afirka fiye da 50 da kuma wakilan ƙungiyoyin yankin.
A jawabin da Ministan Harkokin Wajen Masar ya karanta a zaman taron, el-Sissi ya ce ya kamata muryar Afirka ta kasance a bayyane kuma mai tasiri wajen yanke hukuncin duniya, duba da ƙarfin Ɗan Adam, tattalin arziki, siyasa da yawan alummar nahiyar.
Ya kara da cewa ya dace a sake fasalin cibiyoyin kuɗi na duniya domin tabbatar wa Afirka adalci a wakilci.
Tun shekarar 2005, Ƙungiyar Tarayyar Afirka ke buƙatar a bai wa Afirka aƙalla kujeru biyu na dindindin tare kuma kujeru biyar na wucin gadi a Kwamitin Tsaron Majalisar Ɗinkin Duniya.
Ƙungiyar na ganin hakan zai taimaka wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a nahiyar da ta daɗe tana fuskantar yaƙi.
Sai dai ƙasashen Afirka ba su kai ga matsaya ɗaya kan yadda za a zaɓi wakilan dindindin ɗin ba.