115
Gwamnatin Rasha ta bayyana shirin gina tashar makamashin nukiliya a duniyar wata cikin shekaru goma masu zuwa, a matsayin wani ɓangare na haɗin gwiwa da China wajen kafa cibiyar bincike ta sararin samaniya a can. Wannan shiri na cikin yunƙurin Rasha na farfaɗo da matsayinta a fannin binciken tauraron dan’adam bayan ta fuskanci koma-baya a shekarun baya.
Tun bayan nasarar Yuri Gagarin a 1961 da ya zama ɗan adam na farko da ya shiga sararin samaniya, Rasha ta kasance ginshiƙi a fannin binciken sararin samaniya. Sai dai a ‘yan shekarun nan, ta kasance a baya idan aka kwatanta da Amurka da China, musamman bayan gazawar aikin Luna-25 a watan Agusta 2023 da ya fadi a duniyar wata.
Kamfanin binciken sararin samaniya na ƙasar, Roscosmos, ya sanar cewa ya sanya hannu kan kwangila da kamfanin Lavochkin Association don gina tashar wutar lantarki a duniyar wata nan da shekarar 2036. Hukumar ta ce wannan tashar za ta samar da makamashi ga shirin binciken sararin samaniya na haɗin gwiwa da China, tare da haɗin gwiwar kamfanin nukiliya na Rosatom da Cibiyar Kurchatov.