Home NewsLimamin da ya tseratar da Kristoci a Plateau ya rasu

Limamin da ya tseratar da Kristoci a Plateau ya rasu

Alhaji Abubakar Abdullahi, limamin Yelwa, Gindin Akwati a Barikin Ladi, Plateau, wanda ya yi fice a shekarun baya wajen kare mabiya Kirista daga kisa a rikicin Jos, ya rasu a daren Alhamis bayan fama da rashin lafiya.

Ɗan autan marigayin, Saleh Abdullahi Abubakar, ya tabbatar wa da BBC cewa malamin ya rasu ne da misalin ƙarfe 9 na dare yana da kimanin shekara 90 a duniya.

Saleh ya ce mahaifinsa ya yi fama da rashin lafiya ta ciwon zuciya inda aka kwantar da shi a asibiti a Filato.

“Har an sallame shi bayan jinya a asibiti saboda ya koma gida, sai bayan wajen wata uku zuwa huɗu ne ciwon ya tashi, sai muka mayar da shi asibiti a duba shi a makon da ya gabata, daga nan ne suka sake kwantar da shi wanda daga bisani ya rasu jiya da dare.”

Ɗan ya ce an riga an mayar da gawar shi gida a Yelwa, Gindin Akwati da ke Barikin Ladi domin yi masa jana’iza da ƙarfe biyu bayan sallar Juma’a.

Gwamnan Jihar Plateau, Barr. Caleb Manasseh Mutfwang, ya bayyana jimami kan rasuwar limamin, inda ya bayyana rashin a matsayin rashi ga jihar baki ɗaya.

A cikin sakon ta’aziyyarsa, Gwamna Mutfwang ya bayyana marigayin a matsayin jajirtacce wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai, da kare mutane musamman mata da yara.

Gwamna Mutfwang ya ce rasuwar limamin babban rashi ne babba ga iyalinsa da al’ummarsa, da kuma jihar Plateau gaba ɗaya.

Ɗan marigayin ya mahaifinsa ya ce samu karramawa daban-daban bayan tseratar Kiristoci da ya yi a wani rikicin Jos, ciki har da zuwa hajji sau biyu da kuma lambobin karrama daga gwamnatin Buhari.

Marigayin ya rasu yana da ‘ya’ya 19 da suke raye, ciki har da maza 12 da mata 7, sannan ya auri mata uku inda biyu daga cikinsu sun rasu.

You may also like

Leave a Comment