Home NewsDa ɗumi-ɗumi: 2027 — Ba zan sauka wa kowa ba, Atiku ya sha alwashin tsayawa takara.

Da ɗumi-ɗumi: 2027 — Ba zan sauka wa kowa ba, Atiku ya sha alwashin tsayawa takara.

Da ɗumi-ɗumi: 2027 — Ba zan sauka wa kowa ba, Atiku ya sha alwashin tsayawa takara.

 

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027, yana mai jaddada cewa ba zai sauka wa kowa ba a fafutukar neman tikitin jam’iyya.

 

Atiku ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da magoya bayansa, inda ya ce duk da tsayawarsa kai-tsaye, duk masu neman tikitin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) za su mika kansu ga taron babban zaɓe (presidential convention) domin a tantance cancanta cikin adalci.

 

Ya ce tsarin jam’iyyar ADC ya tanadi gasa ta gaskiya da dimokiraɗiyya, inda kowa zai samu damar gabatar da kansa, amma ya nanata cewa shi Atiku ba zai janye ba.

 

“Na shirya tsaf don fafatawa. Zan shiga gasa a fili, amma ba zan sauka wa kowa ba,” in ji Atiku.

 

Wannan mataki na Atiku na zuwa ne a daidai lokacin da siyasar 2027 ke ƙara ɗaukar zafi, yayin da jam’iyyun adawa ke neman daidaita tsari da haɗin kai domin ƙalubalantar gwamnatin tarayya.

 

A cewarsa, makomar ƙasa na buƙatar shugabanci nagari da gogewa, kuma ya shirya ɗaukar wannan nauyi.

You may also like

Leave a Comment