Home NewsKotu ta yi umarnin a rataye Mansur Garba Rogo bisa samun sa da laifi

Kotu ta yi umarnin a rataye Mansur Garba Rogo bisa samun sa da laifi

Babbar kotun jiha mai 7 ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Amina Adamu, ta zartas da hukuncin kisa ta hanyar rataya akan wani mutum mai suna Mansur Garba Rogo.

Tunda fari dai, Gwamnatin jaha ce ta gurfanar da mutumin bisa zargin kisan kai laifin da ya saɓa da sashi na 221.

Ƙunshin zargin ya bayyana cewar tun a shekarar 2017 Mansur ya soka wa wani abokinsa Ƙaho a Ƙirji, da Wuya, kuma nan take rai ya yi halin sa.

Lamarin ya faru ne a wajen wata farauta da suke zuwa duk lokacin kaka.

Da take karanta hukuncin mai shari’a Adamu, ta ayyana cewar kotun ta gamsu da shaidu 7 da masu gabatar da ƙara suka gabatar.

Bayan kammala hukuncin wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya zanta da kwamishinan shari’a na jahar Kano Barrister Abdulkarim Maude SAN, wanda ya bayyana gamsuwa da hukuncin.

Kotun ta bayyana cewar duk wanda bai gamsu da hukuncin ba zai iya ƙaukaka kara nan da kwanaki 30 masu zuwa.

You may also like

Leave a Comment