Home NewsTinubu ya cire sunan Dakingari a matsayin jakadan Turkiyya

Tinubu ya cire sunan Dakingari a matsayin jakadan Turkiyya

Fadar shugaban Najeriya ta sanar da cire sunan tsohon gwamnan jihar Kebbi, Usman Sa’idu Dakingari a matsayin wanda aka naɗa mukamin jakadan Najeriya a ƙasar Turkiyya.

Wata sanarwa da ta fito daga mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru Bayo Onanuga a jiya Alhamis, ta ce shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin jakadu huɗu da majalisar dattawa ta tabbatar a watan Disamban da ya gabata.

Sanarwar ta ce an naɗa Ambasada Ayodele Oke jakadan Najeriya a Faransa da Kanar Lateef Are zuwa Amurka, da Ambasada Amin Dalhatu, tsohon wakilin Najeriya a Koriya ta Kudu, a matsayin jakada zuwa Burtaniya.

An sanya sunan Dakingari a matsayin jakadan da aka naɗa a Turkiyya.

Amma da safiyar Juma’a, wata sanarwa ta sake fitowa daga fadar shugaban ƙasa inda ta ce “Shugaba Tinubu ya amince da naɗa jakadu uku, amma har yanzu babu jakada zuwa Turkiyya”.

Sanarwar dai ba ta bayar da wani dalili da ya sa ba a sanya sunan Dakingari ba.

Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da shugaba Tinubu ke shirin kai ziyarar aiki ƙasar Turkiyya a ƙarshen wannan makon.

You may also like

Leave a Comment