Home NewsMutum 32 ne sukarasa rayukansu a harin Amurka Shugaban kasar Cuba,

Mutum 32 ne sukarasa rayukansu a harin Amurka Shugaban kasar Cuba,

Mutum 32 ne sukarasa rayukansu a harin Amurka Shugaban kasar Cuba,

 

Gwamnatin ta ce waɗanda suka mutu mambobin sojoji ne da ma’aikatan tattara bayanan sirri, inda aka ayyana kwanaki biyu a matsayin ranakun jimami da zaman makoki na ƙasa baki ɗaya.

 

Ba ta fayyace ainihin rawar da ‘yan Cuban suka taka a Venezuela ba, amma ƙasashen biyu suna da dangantaka ta dogon lokaci, inda Cuba ke ba da tallafin tsaro a madadin mai.

 

Shugaban Cuba, Miguel Diaz-Canel, ya ce ‘yan ƙasarsa suna ba da kariya ga Maduro da matarsa bisa buƙatar Venezuela.

 

Venezuela dai har yanzu ba ta bayyana yawan mutanen da suka mutu yayin harin Amurka da aka kai a gidan shugaban ƙasar Maduro da ke Caracas ba a ranar Asabar.

You may also like

Leave a Comment