Home NewsMatasa huɗu sun samu gurbin zama a gidan gyaran hali a Kano

Matasa huɗu sun samu gurbin zama a gidan gyaran hali a Kano

Kotun majistrest mai lamba 24 da ke zamanta a filin tashi da saukar jiragen sama na Mallam Aminu Kano, karkashin jagorancin mai shari’a Muttaka Abba Dandago, ta sake aikewa da wasu matasa 4 gidan gyaran hali, bisa zarginsu da laifin hada baki da yunkurin garkuwa da mutane, da samu da muggan makamai.

Zargin da ake yi musu ya ayyana cewa, matasan sun zo Kano ne daga jihar Zamfara, inda aka kama su a tashar Kuka ta Kofar ruwa da ke karamar hukumar Dala a Kano, ɗauke da wani buhu da aka samu bindigogi da wasu kayayyaki a ciki.

Matasan da ake tuhumar sun hadar da Buba Usman, Muhammad Abdulrrahman, da Abdullahi Garba, da kuma Usman Umar.

Binciken ‘yan sanda ya bayyana cewa, ana zargin cewa matasan sun shigo jihar Kano ne, domin yin garkuwa da mutane, saboda neman kudin fansa, inda su ka musanta zarge-zargen da ake yi musu.

A yayin zaman kotu na ranar Alhamis 15 ga watan Janairu, 2026, bayan an karanto wa masatan kunshin zargin da a ke yi musu sun musanta, inda mai gabatar da kara ya bayyana wa kotun cewar, har yanzu suna jiran shawarwarin lauyoyin gwamnati kasancewar laifukan da ake tuhumar su da shi ya shiga cikin manyan laifuka.

Kotun ta sanya mako biyu, domin a sake gabatar da matasan gaban kotun domin dorawa daga inda aka tsaya

You may also like

Leave a Comment