Shugaban addinin kasar Iran da kwamandan askarawan kasar sun ja kunnen Donald Trump cewa. Kada yadauka cewa Iran kasa ce ta matsorata.
Suka ce iran ba Venezuela ba ce kuma ba Haiti ba ce ba kuma Panama ba ce, ba kuma wata kasa ce daga yankin latin Amurka ba, Iran kasa ce ta mutanen da suka san kan su.
Suka ce babu ruwan Amurka da duk wani abu da yashafi yan kasar Iran da ke cikin gida.
Yanda baku yarda da tsoma bakin wata kasa ba a lamarin cikin gidan ku. Haka ma Iran bata yarda ba kuma baza ta yarda ba.
Suka ce baza mu firgita ba mu yan kasa ne masu kishin kasar su. Babu wani kurari da zai sa su kaucewa bukatun kasar su don tsoron wata kasa.
Amma idan kuna ganin cin ta, to ga filin nan ta yiwu yakin duniya na uku ne zai faru.
Suka ce tabbas, za mu saukewa Trump abin da yake damun sa ta ko wacce hanya mu da ALLAH muka dogara.